1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasa a jihar Edon Najeriya

Muhammad Bello LMJ
August 6, 2020

Jihar Edo da jama'arta na ci gaba da shiga tsaka mai wuya, da ke da jibi da tashe-tashen hankulan 'yan siyasa masu neman cinye zaben kujerar gwamna da za a gudanar a jihar.

https://p.dw.com/p/3gYQB
Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje zai jagoranci APC, a yakin neman zaben jihar Edo.Hoto: Salihi Tanko Yakasai

Bayan salwantar rayuka da aka fara samu a yanzu, bayanai na nuna cewar an kai wani farmaki na siyasa harabar majalisar dokokin jahar ta Edo, farmakin kuma da ke da nufin sauya shugabancin majalisar. Nan da kasa da makonni shida ne dai ake shirin gudanar da zaben gwamna, kuma a yanzu haka dambarwar siyasar na kara yin zafi. Jam'iyyu 14 ne dai ke fafatawa da juna, ko da yake fafatawar ta fi zafafa tsakanin jam'iyyun APC da PDP.

Gangamin yakin neman zabe da jamiyyun musamman na APC da PDP suka fara dai, ya fara janyo salwantar rayuka tare da jikkata mutane da dama kawo yanzu. Kalaman manyan 'yan takarar biyu, wato Mr. Godwin Obaseki na PDP da kuma Pastor Ize Iyamu na APC, na ci gaba da haifar da zaman dar-dar ga al'ummar jihar da ke shirin jefa kuri'arsu ranar zabe.
Fafatawar neman madafan iko a jahar dai,da dama na ganin fafatawa ce ta a mutu ko ai rai, tsakanin tsohon shugaban Jamiyyar APC na kasa da dama tsohon gwamnan jihar ta Edo ne wato Adams Oshiomhole da kuma gwamnan jihar na yanzu da ke neman wa'adi na biyu wato Godwin Obaseki da su Oshiomhole din suka sa dole ya tsallaka zuwa jam'iyyar PDP.

Nigeria I Adams Oshiomhole
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa kana tshohon gwamnan jihar Edo, Adams OshiomholeHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Wani zaman gaggawa na majalisar jihar ta Edo a baya-bayan nan, ya kai ga bangaren na Oshiomhole tsige mataimakin shugaban majalisar, kuma yunkurin wasu ke kallon mataki ne na neman karbe ragamar majalisar ta karfin tsiya, da nufin cimma burin siyasa da kuma zabe a jihar. Mr Godwin Obaseki shi ne gwamnan jihar ta Edo kuma mai neman wa'adi na biyu a mulkin jihar karkashin jam'iyyar PDP, kuma a hira da na yi da shi ta  waya ya koka kan cewar ya na tunanin jam'iyyar APC za ta yi amfani da karfin mulkin gwamnatin tarayya domin murde zabe, kuma al'amarin da ba za su taba laminta ba.

Hukumar zabe ta kasa dai ,tuni ta ayyana shirinta, na gayyatar 'yan takarar gwamnan na APC da PDP da nufin jan hankalinsu kan bukatar tabbatar da kwanciyar hankula yayin yakin neman zabe da kuma zabukan da ke tunkarowa. A jerin 'yan takarar ta gwamnan jihar ta Edo akwai mata biyu, sannan akwai wasu mata biyu da ke takarar mataimakin gwamna.