1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obi zai kalubalanci sakamakon zabe

Abdourahamane Hassane
March 3, 2023

Dan takarar shugaban kasa a zaben Najeriya da aka yi, Peter Obi, wanda ya zo na uku a zaben. Ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben.

https://p.dw.com/p/4OEz2
Nigeria vor Präsidentschaftswahl Lagos | Kandidat Peter Obi
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Peter Obi ya bayyana cewar zai shigar da kara a gaban kotu a kan sakamakon zaben da dan takarar jam'iyyar da ke yin  mulki Bola Tinubu ya samu nasara. Peter Obi ya bayyana haka  ne a lokacin wani taron manema labarai da ya kira: ''Bani ba, ba ku ba, amma al' umma, da yaran da muke rayuwa tare, ina son mutane su fahimci hakan. zan kalubalanci wannan sakamakon zabe wanda aka yi aringinzo kuri'u a ciki. Tun farko dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya yi korafin cewar an tafka magudi a zaben.