1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan bindiga sun kai hari jihar Imo

Ramatu Garba Baba
April 22, 2023

Yan sanda biyar da fararen hula biyu aka tabbatar sun mutu a sakamakon wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4QQuo
Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da rakiyar jami'an tsaro
Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da rakiyar jami'an tsaro Hoto: David Dosunmu/AP Photo/picture alliance

Rahotanni daga Najeriya sun sheda cewa, wasu 'yan bindiga da ba a kai ga gano ko su wane ne ba, sun hallaka jami'an 'yan sanda biyar da wasu fararen hula biyu a yayin wani hari da suka kai a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar, Mista Henry Okoye, wanda shi ne kakakin rundunar 'yan sandan jihar da ya tabbatar da labarin ya ce, an kai harin ne a ranar Jumma'ar da ta gabata amma ba tare da ya yi wani karin bayani ba.

Jihar Imo kamar sauran jihohin da ke kudu maso gabashin Najeriyar na fama da hare-haren 'yan bindiga da ke lakume rayuka da ma barazana ga zaman lafiya. A baya jami'an tsaron yankin na zargi da ma danganta ire-iren wadannan hare-haren da sa hannun Kungiyar IPOB ta 'yan rajin kafa kasar Biafra, sai dai IPOB din ta sha musanta zargin.