1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane miliyan biyu ambaliya ta shafa a Najeriya

October 16, 2022

Gwamnatin Najeriya ta ce yawan mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar ya karu zuwa mutane miliyan biyu yayin da adadin wadanda suka rasu ya kai mutum 603 a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4IG37
Nigeria I Hochwasser in Kogi
Hoto: Fatai Campbell/AP/picture alliance

Ministar ma'aikatar kula da ayyukan jinkai ta Najeriya Sadiya Umar Faruk ce ta sanar da haka a taron manema labaru da ta gudanar a Abuja.

Ministar ta kuma yi gargadin cewa har yanzu akwai yiwuwar fuskantar ambaliyar har zuwa karshen watan Nuwamba musamman a yankin kudancin kasar, kuma babban abin da suka saka a gaba a yanzu shi ne ceton rayukan jama'a.