1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC: Karancin kudi gabanin zaben 2019

Uwais Abubakar Idris
November 13, 2018

A Najeriya, jinkirin samar da kasafin kudin hukumar zabe don zaben da za’a yi a badi na haifar da damuwa, duk da tabbacin da hukumar ta INEC mai zaman kanta ta bayar cewa ba ta hasashen fuskantar wata matsala

https://p.dw.com/p/38BQ7
Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Hoto: DW/Gänsler

Sauran kwanaki 93 kafin a gudanar da babban zaben na Najeriya da aka tsara yi a farkon shekara mai zuwa. Amma  duk da amincewa da kasafin kudin hukumar na sama da Naira biliyan 189 har zuwa wannan lokaci kudin basu kai ga hannun hukumar ba.

Abin da ya sanya daga hankali a kan illar da wannan zai iya yi. Domin a tsarin zabe akwai matakai har goma sha hudu da aka tsara, ya zuwa yanzu guda biyar ne aka samu cimawa.

A zaben na badi na Najeriyar dai ana da jamiyyu 89 da zasu shiga, kuma sauye-sauyen da aka yi a dokar zabe na iya shafar tsarin aiwatar da shi da zarar an sanyawa dokar hannu, wacce ke gaban shugaban Najeriyar.

Duk da shirin da hukumar zaben Najeriya ke nuna cewa ta yi ga zaben, amfani da na'ura mai aiki  da kwakwalwa wajen tattara bayanai na sanya jefa tambayoyi na shin me hukumar ke yin a tabbatar da kare tsarinta daga masu kutse kamar yadda ya faru a wasu kasashe.