1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Barace-baracen yara na karuwa

Nasir Salisu Zango LMJ
January 22, 2019

Yayin da ake kara samun karuwar kananan yara da ke gararanba da sunan yin bara ko almajiranci musamman a arewacin Najeriya, barazanar tsaro na sanya fargaba.

https://p.dw.com/p/3Bz7Y
Die Bettel-Schüler aus Nordnigeria
Karuwar almajirai a arewacin NajeriyaHoto: DW

Galiban dai ana ganin cewar matukar ba a yi wa tufkar hanci ba, za ta iya zama babbar barazana ga tsaro da ka iya kamo matsalar Boko Haram. Duk da cewar hukumomi a jihar Kano sun yi dokar haramta yin bara musamman ta kananan yaran, amma a yanzu ana kara samun yawaitar kananan yara da ke gararanba a birnin Kano da sunan yin bara. Irin wadannan yara sukan bar inda aka kai su domin karatu su dinga yawo kwararo-kwararo, a wasu lokutan ma sukan kwana a titi ko karkashin gadoji, lamarin da a yanzu ya fara jan hankulan mutane da ke ganin cewar matukar ba a dauki mataki ba, to fa matsalar za ta iya gagarar kowa har ma takan iya gawurta fiye da rikicin Bo ko Haram. 

Major muhd sani tsohon soja ne kuma mai fashin baki kan al'amuran tsaro, ya jaddada cewar matukar al'umma ba su hada kai an tunkari wannan matsalar ba, za ta iya habaka ta hadiye kowa da kowa. To amma ga alama su alarammomi da ke ajiye yaran suna tura su bara ba zasu yadda da duk wani yunkuri na dakile barar ba, domin a koyaushe artabu ake da su suna ganin cewar barar tamkar bangare ne na addini. Alaramma Isma'il Hotoro malami ne mai almajirai, ya ce su ba su yarda da cewar bara ta sabawa addini ba dan haka dole a kyale su su wataya kamar kowa. 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta dade tana kama almajirai sai dai aikin kamen ya fara sanyi. Babban jamian sashen yaki da bara na hukumar Sheikh Dahiru Nuhu ya ce yanayin da suke ganin kananan yaran da ake kawowa bara babban abin tashin hankali ne, wanda a nan gaba zai iya zama babbar masifar da ba a taba gani ba matukar mahukunta ba su dauki mataki ba. Zuwa yanzu dai hankula sun fara komawa kan wannan batu na karuwar almajirai, musamman a birnin Kano inda nan ne ke zaman matattara da ake kawo yara daga sassa daban-daban domin yin barar.