1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Matakan bai wa yara mata kariya a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
October 19, 2023

An fara wani gangami na magance cin zarafin yara kanana ta hanyar gana musu azaba saboda kasancewarsu mata a cikin al'umma a Najeiya, inda 'ya'ya maza kan nuna fin karfi a mu'amalarsu ta yau da kullum da yara matan.

https://p.dw.com/p/4Xly2
Najeriya | Abuja | Cin Zarafi | Yara
An jima ana nuna damuwa kan yadda ake cin zarafin yara musamman mata a NajeriyaHoto: DW/U. A. Idris

Wata sabuwar dabara ce aka bullo da ita a Najeriyar, inda ake mayar da hankali a kan yara kanana maza da yadda suke tasowa a cikin iyali da ma mu'amala a makaranta. A mafi yawan lokuta 'ya'ya maza kan nuna sune kan gaba, wanan ya sanya ko an muzguna da cin zarafinsu ba kasafai suke magana ba. Sanin cewa lamari ne da ya shafi batu na iyali da kulawa da yadda ake taso da yara tun suna kanana a Najeriyar, ya sanya cusa iyayen kasa wato sarakunan gargajiya domin samun nasarar shirin.

An dai kwashe shekaru masu yawa ana magana a kan batun kula da yara mata, kama daga karatunsu da ma yanayin zamantakewar rayuwarsu amma a kan bar batun 'ya'ya maza a gefe guda a kokarin samun nasara ga wannan aiki. Ambasada Sarki Sylvia jami'a a kungiyar Tallafawa Yara Kanana a Najeriyar ta ce, matakin kokari ne na yiwa yaran saiti tun suna kanana. Akwai dai yara 'yan makaranta da suka halarci wannan taro, inda aka yi masu bita ta musamman. Cusa hallaya ta mutunta juna tsakanin yara maza da mata ta yadda namiji zai fahimci cewa kowane jinsi na da muhimmanci ba wai nuna karfi ko cin zalli ba, muhimmin abu ne a kokarin shawo kan wannan matsala.