April 20, 2017
Talla
Al'ummar Najeriya na cigaba da maida martani da ma sharhi kan da matakin da shugaban Najeriya ya dauka na dakatar da sakataren gwamnatin tarayya Babacir Lawal bisa zarginsa da cin hanci da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar Ayodele Oke wanda ya ce wasu kudade da hukumar EFCC ta gano a boye a wani gida mallakin hukumarsa ne. Tuni dai shugaban na Najeriya ya ce ya kafa wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa don gudanar da bincike kana ya basu makonni biyu don gabatar da rahotonsu.