1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mahara sun hallaka sojoji 12

Suleiman Babayo
December 16, 2018

Ana fargabar sojojin Najeriya 12 sun rasa ransu sakamakon fada da mayakan Boko Haram masu dauke da makamai a yankin arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3ADfG
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

Kimanin sojoji 12 sun rasa ransu sakamakon artabu da 'yan Boko Haram masu dauke da makamai a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Kamfanin dillancin labarai Reuters ya ruwaito wasu majiyoyi uku na sojoji na tabbatar da labarin, inda wasu sojojin da dama suka bace bayan gumurzun a jihar Borno. Sojojin sun ce soja daya ya rasa ransa lokacin da suka dakile wani hari daga 'yan na Boko Haram din cikin dare Jumma'a a wata karamar hukuma.