1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Lauyoyi na so a binciki kalaman Bulkachuwa

Uwais Abubakar Idris
June 16, 2023

Takadama ta kaure bayan kalaman tsohon sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa cewa ya sa baki matarsa ta taimaka wa abokan aikinsa ‘yan majalisa wajen shari'a a kotu

https://p.dw.com/p/4ShTo
Nigeria | Bildungskosten | Universität Abuja
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Kalaman da Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ya yi a zaman karshe na majalisa ta tara sun janyo cece-kuce a Najeriyar, domin tun a lokacin da yake jawabi sai da tsohon shugaban majalisar dattawan Sanata Ahmed Lawan katse jawabin. Bayanan da sujka haifar da cece-kuce.

Tuni kungiyar lauyoyin Najeriya ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare sashin shari'a don haka shugaban kungiyar Yakubu Maikyau ya rubuta wa sifeto janar na ‘yan sandan Najeriyar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa su yi bincike a kan wannan batu da masu sharhi ke cewa abin boye ne ya fito fili. Sai dai Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ya ce akwai bukatar a fahimci abinda yake nufi domin katse hanzarinsa aka yi kafin ya kamala jawabi.

A yayin da ake ci gaba da mayar da martani, za a sa ido a ga tasirin bayanan da tsohon sanatan ya yi a kan abinda yake nufi da matakin da hukumomin da aka nemi su bincika za su dauka a kan batun.