1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IPOB ta yi amai ta lashe game da zaben Anambara

Muhammad Bello MNA
November 5, 2021

Al'amura sun daidaita a jihar Anambara da ke Kudu maso gabashin Najeriya game da zaben da ake ta fargabar ba zai yi wu ba bisa dalili na tashin tashinar 'yan rajin Biafra na kungiyar IPOB.

https://p.dw.com/p/42ePs
Nigeria Regionalwahlen 2019
Hoto: Reuters/A. Sotunde

An dai ta samun dauki ba dadi tsakanin kungiyar 'yan aware don kafa kasar Biafra ta IPOB da kuma gwamnatin Najeriya ta hanya arangama da dakarun tsaron kasar da suka hada da na soji da 'yan Sanda a yankin Kudu maso gabashin Najeriyar, inda kuma aka yi ta samun salwantar rayuka.

'Yan bindigar da ake cewar ba a sansu ba a yankin da kuma ake ta zargen 'yan IPOB din ne, sun ta da hankula ta hanyar kai hare-hare ga jami'an tsaro da ma fararen hula a yankin tare ma da haifar da tsaikon al'amuran yau da kullum duk ranar Litinin, inda suke ikirarin sai an sako musu jagoransu Mr Nnamdi Kanu, kuma ma ta kai sun yi ta ikirarin ba za su bari a gudanar da zaben kujerar gwamna ta Anambara ba da INEC ta ce ta shirya gudanarwa.

Gwamnatin Najeriya ta kai dubban jami'an tsaron soji da 'yan sanda a jihar Anambara
Gwamnatin Najeriya ta kai dubban jami'an tsaron soji da 'yan sanda a jihar AnambaraHoto: Nasu Bori/AFP/Getty Images

Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar akwai zabe tare da kai dubban jami'an tsaron soji da 'yan sanda jihar ta Anambara, inda bayan jami'an tsaron sun ta yin atisayen sai kwatsam kungiyar ta IPOB ta sanar da janye umarnin zaman dirshan a gida da ta bai wa al'ummar ta Anambara me nufin kada kowa ya fito zaben na wannan Asabar. Janye wannan umarni dai da alamu ya sauya yanayi a jihar a yanzu a cewar  mai magana da yawun rundunonin tsaron aiki a yayin zaben, DSP Nwode Nkiruwa.

"Ina tabbatar da cewa mun shirya tsaf ta bayar da tsaro, kuma muna ta gaya wa mutane kan su fito zabe komai lafiya lau tare kuma da gaya musu dokokin da za su kiyaye in sun fito din."

Magoya bayan kungiyar IPOB yayin  wata zanga-zangar da suka yi a birnin Fatakwal
Magoya bayan kungiyar IPOB yayin wata zanga-zangar da suka yi a birnin FatakwalHoto: Getty Images/AFP

To sai dai fa dattawa da kuma gwamnoni gami da wasu ma su fada a ji a yankin na Kudu maso gabashin kasar sun ta fadin cewar ba tun yau suke ta tattaunawa da 'yan kungiyar ta  IPOB ba, kan a kai zuciya nesa, tare da barin a yi wannan zabe. Sai dai mutane a yankin da ma a wasu sassan kasar na ganin cewar firgici ne ya kama kungiyar ta IPOB ya kai ga sauya matsayinta, ganin yadda jami'an tsaro suka kasa suka tsare a jahar ta Anambara tun kusan kwanaki uku.

Tuni dai hukumar zabe ta kasa INEC ta nunar cewar ta fara rarraba mahimman kayayyakin zabe da suka hada da na'urar tantance masu kada kuri'a da takardar zabe da takardar zana sakamakon zabe da sauransu.

Akwai dai kananan hukumomi 21 a jahar ta Anambara da jam'iyyu 18 da suka hada da PDP da APC da ake ganin za su fi fafatawa a zaben.

An yi wani zama da 'yan takarar inda aka cimma wanzar da zaman lafiya yayin zabgen da kuma bayansa.