1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan inganta wutar lantarki a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
March 12, 2020

Martani kan tanadin dauri na shekaru goma ga wanda ya saba dokar haramta shigo da Janaraito Najeriya a kokarin inganta samar da wutar lantarki bisa kudurin da majalisar datawan ke aiki akai.

https://p.dw.com/p/3ZHjp
Nigeria Strom Elektrizität Energie Generator Lagos
Hoto: picture-alliance/dpa

Ci gaba da tabarbarewar harkar samar da wutan lantarki a Najeriya duk da makuddan kudaden da ake zubawa wannan sashi da ya kai ga cefanar da wasu sassansu a hannun ‘yan kasuwa, ya sanya gabatar da wannan kuduri. Dokar da suke hasashen zata taimaka bunkasa harkar wutar lantarki a Najeriyar Sanata.

To sai dai tuni lamarin ya sanya maida martani daga ‘yan Najeriya da dama, sanin cewa an fi dogaro a kan  Janaraito fiye da kamfanin wutar lantarki na kasar duk da mayar da shi hannun ‘yan kasuwa.

Ta dai ta kaiga hatta majalisar dokokin Najeriya na kasafta makuddan kudade wajen shigo da Janaraito a kasar, amma  ga Injinya Ahmed Zakari Nguroje wanda kwararre ne a wannan fanin ya ce  a hasashensa akwai amfani ga wannan.

Ta dai kaiga gwamnatin kurarin na amshe harkar wutar lantarkin daga kamfanonin kasar saboda gazawarsu da ma zargi na makarkashiya, domin daga cikin megawatt dubu 13 da ake samarwa dubu uku ne suke iya saye su rarrabawa ‘yan Najeriya abinda ke haifar da zargi na makarkashiya.