Taro kan rufe kan iyakar Najeriya
November 14, 2019Kasashen guda uku sun kwashe sao'i shida suna tattaunawa a kan wannan batu da ya kai wa kasashen da ke makwataka da Najeriyar iya wuya, abin da ya sanya suka yi tataki zuwa da kai da yafi sako na kalamai da bayanai, domin shawo kan Najeriyar a kan batun rufe kan iyakokin nata. A karshen taron dai sun cimma matakai 13 da za su dauka. Muhimmi daga ciki shi ne na kafa rundunar sintriri ta hadin gwiwa tsakanin kasashen uku, wacce za ta kama duk wadanda aka samu da fasa kwabrin kaya a kan iyakokin.
Fusata kan rufe iyakoki
Su dai ministocin kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin sun bukaci Najeriyar ta bude kan iyakokin nata ne ba tare da wani bata lokaci ba, bukatar da ba su samu ba. A wata alama da ke nuna fusata a fili, ministocin sun fiice tun kafin a kammala taron. Bazoum Mohamed shi ne minsitan kula da harkokin cikin gida na Nijar da tun da farko ya bayyana cewa.
"Najeriya ta dauki mataki mai zafi na rufe kan iyakokinta da kasashenmu bisa abin da ta kira matsalolin da take fuskanta na fasa kwabri, mu ma kanmu wannan matsala na shafarmu, hakan yasa muka taru domin lalubo mafita wacce ba za ta cutar da kowanenmu ba. Hakika matsalar fasa kwabri matsala ce da ta addabi kasashenmu duka."
ECOWAS za ta shiga tsakani
Taron dai ya yi amanna da kalubalen fasa kwabrin kaya da ma shigar da makamai ta kan iyakokin kasashen. Tun da farko kwamshinan kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS mai kula da ciniki da hana fasa kwabri da kuma da shige da ficen al'umma Tei Konzi ya ce kungiyar za ta tabbatar da sulhunta matsalar.
"Ina son in tabbatar maku da cewa kungiyarmu ta ECOWAS a shirye take ta bayar da gudummawa domin kawo gyara ga matsalolin da suka shafi ko suka addabe mu gaba daya."
Tuni 'yan kasuwar Najeriya musamman masu harkar man fetir ke kira ga kasashen da dukkaninsu ke cikin ECOWAS din da su duba lamari. Taron dai na nuna daura dambar na daukar matakan da za su kai ga bude kan iyakokin Najeriyar musamman tsakaninta da Nijar da kuma Jamhuriyar Benin.