1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba ma goyon bayan ballewa daga Najeriya - Ijaw

June 24, 2021

A wani abun dake karfafa gwiwar gwamnatin Najeriya dake yakar yunkurin tsagerun 'yan kudu maso gabashin kasar, kabilar Ijaw dake zaman mafi girma a yankin Niger Delta tace bata goyon bayan ballewa daga Najeriyar.

https://p.dw.com/p/3vWNA
Nigeria Abuja | Prsident Muhammadu Buhari ernennt Ibrahim Gambari zum Stabschef
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Reuters/Nigeria Presidency

Tarrayar Najeriyar dai na takama da yankin Ijaw wajen mafi yawan man fetur da kasar ke dogaro dashi wajen rayuwar yau da gobe. Kuma kama daga sarakuna zuwa ga shugabanni kabilar dama uwa uba matasan na Ijaw basu boye goyon bayansu ga cigaban kasar wuri guda ba wajen wani taron da suka gudanar da shugaban kasar a Abuja.

Wakilan na Ijaw dake tozali da shugaban kasar tun bayan sake tashi na fatalwar Biafran dai sun ce sun iso Abujar ne da nufin goyon baya ga cigaban kasar wuri guda duk da barazanar a ware dake tashi da lafawa a kasar a halin yanzu. Farfesa Benjamin Ogele na zaman jagoran tawagar da ko baya na matasan ta kuma kunshi sarakuna da sauran shugabanni kabilar ta Ijaw.

Nigeria, König Plaintiff
Basaraken kabilar Ijaw a Jihar Bayelsa ta NajeriyaHoto: George Osodi

Muna faiyyacewa a fili domin duk masu tunanin ballewa da su ji cewar kada su fara tunanin hada duk wani bangare na al'ummar kasar Ijaw a tunaninsu. Ba zamu balle zuwa wata kasa ba. Ba zamu bar wani yanki namu ya je wani wuri ba, zamu cigaba da kasancewa a Najeriya guda daya. Shugaban kasa a yayin da muke yi maka godiya ga wannan dama da ka bamu da kuma taimakon da kake mana, zamu so ka cigaba da bada damar tattaunawa da zata bada damar gina ingantattciyar Najeriya abar alfahari ga kowa

Goyon bayan na Ijaw dai daga dukkan alamu na shirin ya kara karfafa gwiwa ga Abujar dake neman kai karshen tsgerancin dake ta ruruwa a yankin na Kudu maso gabas. Abujar dai na kallon zawarcin na Ijaw dake zaman kabila mafi yawan al'umma a cikin yankin Niger Delta masu arzikin man fetur na iya kaiwa ga tabbatar da zaman lafiya cikin yankin da kasar ke takama da shi wajen harkokin yau da na gobe. Kuma shugaban kasar bai boye ba wajen nuna farin cikinsa da matsayin kabilar dake samar da kudin da kusan kowa ke wadaka a ciki.

Nigeria | Schwere Explosion in Lagos
Kokarin kashe gobara daga bututun maiHoto: Reuters/T. Adelaja

Ina farin ciki da sake jaddada imaninku ga hadaddiyar tarrayar Najeriya. A lokacin da kuke tare da ni, ina rokon ku da amfani da damarku wajen ganin mun yi aiki tare wajen tabbatar da kasarmu ta zama hadaddiya ta yadda zamu tunkari matsalolinmu tare. Kuma mu warware kalubalemu tare.

Ko bayan batun hadin kai daga dukkan alamu muhimmiyar matsalar dake tsakanin Abuja da matasan yankin Niger Delta na zaman fashin bututu da tsayar da harkokin hakar mai, kalubalen kuma da a cewar Garba Shehu dake zaman kakakin shugaban kasar bai boye ba yayin ganawar.

Najeriyar dai na tsakanin hadewa wuri guda domin tunkarar matsalolin tattali arziki dake tarnaki ga makoma kasar ko kuma cigaba da kace nace da ake kallo na dada dakushe kokarin 'yan kasar na bada gudumawar gina kasa.