1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar shari'ar Emefiele a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 23, 2023

Kotun da ke sauraron shari'ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar tare da tsarewa Godwin Emefiele ta yi zamanta, ba tare da ambato shari'ar tasa ko kuma bayyana ranar da za a sake sauraron karar ba.

https://p.dw.com/p/4VVyO
Najeriya | Godwin Emefiele | Cin-Hanci
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin EmefieleHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Ana dai tsammanin tsohon gwamnan babban bankin Najeriyar da aka dakatar Godwin Emefiele ya shigar da bukata a gaban kuliya, sai dai bai bayyana a zaman kotun ba haka ma ba a bayyana kararsa cikin kararrakin da kotun za ta saurara ba. Emefiele dai, na fuskantar tuhuma har guda 20 da suka hadar da almundahana da kuma yin amfani da mukaminsa na gwammannan babban bankin Najeriya ba bisa ka'ida ba.