1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hankula sun koma kan zaben jihar Kano

Yusuf Bala Nayaya AMW, AMK, FM, ZUD
March 10, 2019

Daga sassan dabam-dabam na Najeriya hukumomin zabe sun kwana ana aikin tattara sakamakon zaben sai dai a Kano 'yan sanda sun kama mataimakin gwamna da kwamishina saboda zargin tada hatsaniya.

https://p.dw.com/p/3EjYF
Nigeria Präsidentschaftswahlen
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Yayin da aka shiga dako na sakamakon zaben gwamnoni na jihohi 29 a Najeriya. A can jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya kuwa yayin da ake tsammanin sakamakon karshe zai bayyana wasu manyan jami'ai na gwamnati da suka hadar da mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo an zarge su da yunkuri na tada hayaniya, lamarin da ya sanya jami'an 'yan sanda na jihar suka kama su.


An shiga fargaba a jihar Rivers da ke a kudancin Najeriyar sakamakon tsayar da aikin tattara sakamako bayan da hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta bayyana cewa jami'an ta na fuskantar barazana. 

A Bauchin Najeriya za a sake wasu zabukan. A jihar Katsina kuwa Aminu Bello Masari na jam'iyyar APC ya lashe zaben gwamna a cewar Farfesa Abdullahi Abdu Zuru babban jami’in zabe a jihar. Za'a sake yin zaben gwamna a wasu yankunan da aka soke zabe jihar Plateau da suka hada da Barikin Ladi da Bassa da Bokkos da Jos ta Arewa da Kanem. Babban jami'in zaben jihar Farfessa Richarch Anande, ya sanar da hakan da safiyar Litinin dinan a Jos.

Da karfe 3:45 na safe Litinin din nan ce aka kawo karshen tattara sakamakon zabe a jihar Adamawa,sai dai jami'in da ke tattara sakamakon Farfesa Andrew Haruna bai bayyana dan takara da ya lashe zaben ba saboda rashin kammalar zaben kamar yadda doka ta tanada.