1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gini ya fadi a jihar Legas

Binta Aliyu Zurmi
October 12, 2020

Rahotanni daga jihar Legas da ke kudancin Najeriya na cewar an samu rushewar wani gini a yankin Ikoyi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8 maza 6 mata biyu yayin da wasu mutum 10 suka sami munanan raunika.

https://p.dw.com/p/3jouH
Nigeria Gebäudeeinsturz in Lagos
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Hukumar da ke kula da ababen hawa a Legas ta Lesama ce ta fidda wannan sanarwar a  jiya Lahadi bayan aukuwar hadarin.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga sanin takamaimai dalilin rugujewar ginin ba, amma hukumar ta Lesama da wasu hukumomi a jihar na kokarin gano dalilin faduwar ginin. Ana yawan samun faduwar gini a jihar ta Legas inda cinkoson alumma ke rayuwa a gine-gine marasa inganci.

ko a watan Maris din shekarar nan an sami faduwar wani bene da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 da yawancinsu kananan yara ne 'yan makaranta.

Daga shekarar 2014 zuwa yanzu an sami asarar rayuka sanadiyar faduwar gini na sama da mutum 250 a Legas.