1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Jama'a sun gudu bayan ficewar sojin Chadi

Gazali Abdou Tasawa
January 4, 2020

Daruruwan 'yan Najeriya mazauna garuruwan iyaka da Chadi sun tsere daga garuruwansu bayan da sojojin kasar Chadi da ke yaki da Boko Haram a yankin suka fice daga yankin a ranar Juma'ar.

https://p.dw.com/p/3ViXT
Soldaten aus dem Tschad Archiv 2014
Hoto: AFP/Getty Images/M. Medina

Daruruwan 'yan Najeriya mazauna garuruwan Gajiganna da Monguno da sauran garuruwan kusa da iyaka da kasar Chadi sun tsere daga garuruwan nasu a ranar Juma'a zuwa Maiduguri, bayan da sojojin kasar Chadi da ke yaki da Boko Haram a yankin suka fice daga cikinsa a ranar Juma'ar. Watanni tara da suka gabata kenan da kasar ta Chadi ta girke sojoji dubu 12 a garuruwan Najeriya na kan iyaka da ita, da zimmar yaki da Boko Haram.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa an gano sojojin kasar ta Chadi a cikin tankokin yaki da sauran motoci sun ratsa gadar da ta raba biranen Kousseri na Kamaru a kan hanyarsu ta komawa gida Ndjamena.

Kakakin rundunar sojin kasar ta Chadi Kanal Azem Bermandao ya ce a yanzu babu sojin Chadi daya a Najeriya, sun fice bayan da wa'adin aikinsu ya cika, inda yanzu za su koma sansanoninsu da ke a yankin tafkin Chadi. Wani dan kato da gora a birnin na Mungono da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce suma sojojin Najeriya da ke aiki da na Chadi a yankin sun fice daga cikinsa.