1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna

November 22, 2021

Al'ummar arewacin Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan yadda 'yan bindiga suka halaka tsohon dankarar gwamnan jihar Zamfara, tare da yin awon gaba da matafiya da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

https://p.dw.com/p/43L1I
Nigeria Abuja | Proteste | Entführte Studenten
Al'ummar Najeriya na yin zanga-zangar adawa da rashin tsaro a kasarHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Rahotanni dai sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da dimbin matafiya a hanyar ta Kaduna zuwa Abuja. 'Yan bindigar dai sun tare matafiyan ne a garin Rijana, inda bayan harbe-harbe da manyan bindigogi masu garkuwa da mutanen dan neman kudin fansa suka halaka tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfaran a zaben 2019 da ya gabata Alhaji Sagir Hamisu. Wannan lamari dai ya sanya Zamfarawa mazauna Kaduna nuna rashin jin dadinsu, kan tabarbarewar tsaro a kan wannan hanyar. Sun kuma yi kira ga gwamnati kan ta kara himma wajen kawo karshen ayyukan 'yan bindigar.