1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece-kuce kan tallafin iyalai

Abdullahi Tanko Bala
July 20, 2023

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake nazarin shirinta na tallafa wa iyalai miliyan 12 da Naira 8,000 har na tsawon watanni shida. Wannan dai lamari ne da wasu a kasar ke ganin yana da bukatar gyara.

https://p.dw.com/p/4UCUt
Hada hadar Jama'a a jihar Lagos a Najeriya
Hada hadar Jama'a a jihar Lagos a NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

Sakamakon tashin farashin mai da ya rubanya bayan janye tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi, shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kudirin gwamnati na tallafa wa iyalai matalauta da kudi Naira dubu 8,000 domin rage musu radadin tsadar rayuwa. 

Sai dai kuma matakin ya janyo cece-kuce da martani mabanbanta daga yan kasar.