1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maratani kan sabon farashin man fetur a Najeriya

Nasir Salisu Zango SB/ZMA
July 18, 2023

Karin farashin litar mai ya kara jefa jama'a cikin rudani sakamakon tsadar da ake ci gaba da fuskanta a Najeriya lamarin da ake gani zai shafi sauran kayayyakin bukatun rayuwa.

https://p.dw.com/p/4U5sJ
Najeriya | Gidan sayar da man fetur a birnin Lagos
Gidan sayar da man fetur a birnin Lagos da ke NajeriyaHoto: DW

Mutane a Najeriya sun wayi gari da wani sabon karin farashin man fetur, wanda ya girgiza galiban talakawa da masu matsakaicin samu a fadin kasar, ba dadewa ba ne Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana janye tallafin man fetur a kasar wanda nan take ya sa farashin kowacce lita ya koma naira 550, sai dai ana tsaka da kukan wannan karin farashi wanda ya ninka sau biyu sai kuma gashi an sake wayar gari da sabon kari inda aka fara sayar da man zuwa ranar 617 kowacce lita lamarin da ya kara jefa jama'ar kasar a cikin Rudani.

Karin Bayani: Cire tallafin mai ya haifar da cece-kuce a Najeriya

Najeriya I Gidan sayar da man fetur a birnin Abuja
Gidan sayar da man fetur a birnin Abuja na NajeriyaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

An wayi gari da karin farashin mai zuwa naira 617 a wasu wuraren ma 620,ya zama wani babban lamari da ya jefa al'ummar Najeriya cikin tashin hankali da rudani, a Jihar Kano dai tuni wasu gidajen mai suka juya lita 'yan kalilan da ke sayarwa a kan tsohon farashi na naira 550 kuma tuni an fara samun dogon layi na masu bukatar sayen man.

Wannan mataki ya kara jefa al'ummar kasar cikin tashin hankali bama ga masu rangwamen gata ba hatta ga masu matsakaicin karfi yanzu haka kuka suke dangane da yadda wannan sabatta juyatta da ake yi da talakawan kasar ke daukar sabon salo. Barrista Abba Hikima Fagge lauya ne a Kano da ke cewar hakika talaka ya fara kasa gane gabas a Najeriya.

Najeriya I Gidan sayar da man fetur a birnin Abuja
Gidan sayar da man fetur a birnin Abuja na NajeriyaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Dilallan man fetur a Nigeria dai sunce wannan kari fa somin tabi ne matukar farashin dala zai ci gaba da tashi dan haka dole mutane su shirya, Alhaji Adamu Mai Kifi guda ne daga cikin dillalan man fetur a Kano, ya ce matukar ana neman mafita to dole a samu hanyar da kasar za ta ringa samar da man fetur din ta a cikin gida.

Yanzu haka dai galiban mutane musamman masu matsakaicin hali sun fara bayyana matakan ajiye motocin su da komawa taka sayyada ko kuma hawan babur, lamarin da ke kara bayyana wani samfurin juyin-juya halin tsuke bakin aljihu.