1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani kan yaki da COVID-19 a Najeriya

May 19, 2020

A wani abu da ke zaman barazana mai girma, ana ci gaba da samun takun saka a tsakanin gwamnatin tarayyar da ke fadin a tsaya a matakai na kariya, da kuma jihohin da ke sauyin matsayi a cikin yakar annobar COVID-19.

https://p.dw.com/p/3cTeS
Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/Fotostand

Kama daga jihar Kano zuwa takwararta ta Borno da ma Adamawa da can a jihar Ondo dai, jihohin Tarayyar Najeriyar kusan guda bakwai ne dai ya zuwa yanzu suka ayyana bayar da damar  harkokin addini ko bayan na kasuwa, a wani abu da ke zaman bijirewa umarnin kwamitin yakar cutar na kasa. Kuma na kan gaba a cikin sabon tsarin na a bude dai, na zaman matsin lamba ta malaman manyan addinan kasar guda biyu da ke kallon ci gaba a cikin tsarin zaman gidan ya saba ga kasar da ke daf da fuskantar bukukuwan Karamar Salla.

Ko a Kano dai alal ga misali, gwamnatin jihar ta ce ta dauki matakin  bayar da damar salla ta Jumma'a da ma yin Idi a jihar ne domin biyan bukatar wasu gungun malamai da suka ziyarci gwamnan jihar. Mallam Muftahu Yahya malami ne a Abuja da kuma ya ce komawa zuwa ga mai dukan na zaman babbar mafita a cikin annobar da ke ta kara yaduwa, maimakon ci gaba da zama cikin gidan da ba shi da tasiri ga rayuwar al'umma.

Nigeria Ramadan
Bude wuraren ibada a NajeriyaHoto: picture-alliance/AA/M. Elshamy

In har bude Majami'u da Masallatai na iya kai wa ga biya na bukata, tarihi dai kuma a fadar Mallam Hussaini Zakariya da shi ma ya kasance malami a Abuja, ya nunar da cewa gujewa annobar na kan gaba da 'yancin addinin. Ko dai wace hanya ake shirin da a dauka a tsakanin tarayyar da ke neman tunkarar matsalar da baki daya da ma jihohin da ke nema na biyan bukata ta wasu, ga Auwal Mu'azu da ke sharhi a cikin lamura na kasar, abin da ke faruwa a jihohin a halin yanzu, na zaman kokari na kaucewa turjiyar al'umma da suka share lokaci cikin gida.

Kimiyya dai a fadar Ibrahim Kana da ya kasance likita a ma'aikatar lafiyar kasar, ya nuna karuwa ta yamutsi wuri gudan ko dai a cikin sunan addinin ko a kasuwa, na nufin karuwar barazanar yaduwar cutar cikin kasa. Sai da ta kai ga shi kansa shugaban kasar tsoma baki da nufin daukar hankalin gwamnonin da ke ta yin gaban kai cikin kasar da annobar coronavirus din ke barazanar yaduwa cikin lungu da sako.