1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Artabu tsakanin 'yan Shi'a da sojoji

Abdourahamane Hassane
November 1, 2018

Mutane da dama ne aka kashe a zanga-zangar da 'yan Shi'a suka yi yayin da wasu daruruwan suka jikkata.Sannan har yanzu ana ci gaba da yin tababa tsakanin jam'ian tsaro da 'yan Shi'ar a game da adadin wadanda suka mutu.

https://p.dw.com/p/37Vhm
Nigeria Abuja Proteste von Schiiten des Islamic Movement
Hoto: picture-alliance/AA/A. A. Bashal

Zanga-zangar wacce 'yan Shi'ar suka kwashe kwanaki uku suna yi domin tilasta wa gwamatin sako jagoran kungiyar Sheik Ibrahim Zakzaky, wanda ake tsare da shi a gidan kurkuku kusan shekaru uku. Yanzu haka  ta saka jama'a cikin zaman fargaba na abin da ka iya biyo baya a Najeriyar, Bayan rikicin Boko Haram da kuma na sauran rigingimun da aka yi ta fama da su a baya.'Yan Shi'ar dai sun ce an kashe musu mutane sama da 49 yayin da jami'an tsaron ke cewar mutum shida ne kawai aka kashe.