1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin aikin yi ya ragu a Najeriya

August 27, 2023

Hukumar kiddigar Tarrayar Najeriya ta ce Rashin aikin yi ya ragu cikin kasar ya zuwa Kaso 4.1 a karon farko na shekara da shekaru.

https://p.dw.com/p/4VayE
Mun yi amfani da tsohon hoto
Mun yi amfani da tsohon hotoHoto: Nic Bothma/EPA-EFE

Wani rahoto na hukumar dai ya ce masu fama da rashin aikin dai sun sauko daga kaso 33 da suke a farko na shekara ta 2020 ya zuwa kaso 4.1 a farko na wattani uku na shekarar bana. Sabuwar kiddidigar dai daga dukkan alamu na shirin dadada rai na masu mulki na ksar da ke da alkawari na fidda 'yan kasar cikin  rashin aikin yin. Hukumar  dai ta ce ta fitar da sabo na  ma'auni da ya sauya tsarin aiki cikin kasar tare da nasarar rage rashin aikin yi.  Akasin kiddidigar da ke fadin mutane miliyan 133 cikin kasar na rayuwa ciki na talauci, hukumar ta ce Duk wani mai aiki ko da na nawa guda cikin naki dai to yana cikin masu aiki na kasar. Kaso  92 cikin Dari na masu aikin Tarrayar Najeriya na zaman na kananan da ke zaman na kashin kansu. Sabuwar kiddidgar dai na zuwa ne a lokacin da batu na zare tallafin man fetur dama daidaito na farashi na dala ke dada jawo wayyo Allah tsakanin miliyoyi na 'yan kasar da ke fadin ta lalace. Murtala Aliyu dai na zaman sakatare na kungiyr dattawan arewacin Tarrayar Najeiryar ACF da ke ta kokari na kare muradun miliyoyin al'ummar arewacin kasar. Kuma ya ce abun da ke cikin kasa a halin yanzu bai kama da sakamakon kiddidgar da ke dada nuna alamun sauyi na rayuwar al'ummar yankin ba.

Siyasa ko gaskiyya zance batun na samu raguwar masu zaman kashe wondo a Najeriya

Masu neman aiki a Abuja Najeriya
Masu neman aiki a Abuja NajeriyaHoto: Thomas Lohnes/epd/imago images

kokari na yaudara ko kuma inganta rayuwa, akwia dai tsoron sabuwar kiddidigar na iya komawa kafa ta siyasa a tsakanin 'yan mulmki na kasar da kila ma a adawa. Batun na aikin yi dai na zaman na kan gaba tsakanin jam'iyyun kasar da ke neman iko a lokaci mai nisa. To sai dai kuma a tunanin Dr isa Abdullahi da ke zaman kwarrae ga batu na tattali na arzikin, alkaluman kiddidgar na da babban burin fargar da masu mulki na kasar ne maimakon bakar siyasar gado. Sama da mutane miliyan 133 ne dai hukumar kididdigar ta ambato da talauci mai nisa cikin kasar da ke da arziki amma kuma ke kukan babu. Kuma alkawura na gwamnatocin baya na samar da aiyyuka tsakanin al'umma na shirin karewa a takarda maimakon gidaje da kila ma aljihun talakawa na kasar.