1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa na ci gaba da ta'adi a Najeriya

October 21, 2019

Ambaliyar ruwa a gabar tafkin Chadi ya haifar da ambaliyar ruwa da ya lalata daruruwan gidaje da gonaki sama da 2000 a wasu kauyuka takwas da ke arewacin jihar Borno a Najeriya. 

https://p.dw.com/p/3RdhG
Nigeria Tschadsee-Region Fluten
Hoto: DW/A. A. S. Muhammad

Daruruwan mutane na cikin yanayi na neman mafaka da tsananin bukatar abinci a yankin arewacin Borno da ke Najeriya sanadiyyar ambaliyar ruwa da ta lalata daukacin gidaje da gonakinsu. Garuruwan Dusuman da Kachallari na daga cikin kauyukan da wannan ambaliyar ruwan ta yiwa mumunan barna, gonakin sun kasance tamkar koguna, a yayin da jiragen kwale-kwale ke zaman abin da jama'a ke amfani da shi don shiga garuruwan da kuma gonaki, wasu manoma da suka yi hira da wakilin DW sun bayyana bacin ransu da takaici game da ambaliyan, tare da nuna cewa suna cikin yanayi na tashin hankali ganin yadda a gabanin ambaliyar mutanen yankunan sun karbi tallafin bashin noma daga babbankin Najeriya lamarin da ya kara jefa su cikin rudani.

Baya ga matsalar ambaliyar ruwa da akwai batun tabarbarewar tsaro da tun daga farko ta hana dubban manoma zuwa gonakin, wani manomi a garin Dusuman ya shaida wa DW halin da suke ciki inda ya ce lamarin ya kara ta'azzara rayuwarsu a yankin, a daidai lokacin da hukumomi ke cewa za su yi iyakacin kokarinsu don magance matsalar ambaliyan ruwa da kuma karancin abinci, inda kwamishinan kula da ayyukan gona na jihar Borno Injiniya Bukar Talba ya ce "sun yi tanadin kayan tallafi ga manoman domin inganta noman rani ta yadda za a cike gurbin da suka matsalar cimaka da suka fuskanta a damuna." 
Masana sun bayyana fargabar samun matsanciyar yunwa saboda lalacewar gonaki da ambaliyar ta haddasa musamman ganin matsalar tsaro ba ta bari aka yi noma a wasu gonaki da dama ba. a daidai lokacin da rufe kan iyakokin Najeriya ke ci gaba da haifar da rashin samun wadattacen abinci a yankunan da ke kan iyaka da wasu kasashe.