Nageriya: Barazanar karin matalauta miliyan 13
January 24, 2025A yayin da masu mulkin tarayyar Najeriyar suke fadin an kare hawa, wata cibiyasa da ke bin diddigin tattalin arziki a duniya ta ce, wasu kari na 'yan kasar miliyan 13 na shirin fadawa kogi na talauci a shekarar bana ta 2025.
Can cikin batu na takarda dai tarayyar Najeriyar tana shirin kallon girma a shekarar bana sakamakon tasirin manufofi na tattalib arziki na masu mulki na kasar. Babban bankin kasar na CBNdai alal ga misali ya ce kasar za ta kalli karuwar da ta kai sama da kaso hudu a cikin 100 a shekarar da ke zaman gada a tsakanin gwamnatin kasar da da siyasa ta shekara ta 2027.
To sai dai kuma wata cibiyar da ke bin diddigi na tattali na arziki a duniya dai ta ce akasi na tunanin babban bankin, 'yan kasar da ke shirin amsa kira na talauci na shirin su karu a shekarar banan. Kuma a fadar Pricewatercoopers Najeriyar za ta samu karuwar talakawan da kusan mutane miliyan 13 a banan sakamakon hauhawa ta farashin dake ta karuwa cikin kasar a halin yanzu.
An dai kare shekarar tare da hauhawar kaiwa kaso 34.8 adadi mafi yawa cikin tarihi na shekara da shekaru. Tuni dai sabuwar kiddidigar ta fara jawo muhawara mai zafi a cikin tarayyar Najeriya a tsakanin masu adawar dake fadin an kasa, d akuma masu gwamnatin dake fadin ana bisa hanya.
Adadin dai na shirin kara yawan matalauta daga miliyan 113 ko kuma kaso 40 cikin dari na daukacin al'umma ta kasar, abun kuma da ke shirin dora aya ta tambaya bisa manufofi na tattali na arzikin kasar. Zare tallafin man fatur, ko bayan karin kudin wata dama kyale Naira goga kafada cikin neman daraja ne dai ake ta'allakawa da shiga ni'yasu a bangaren miliyoyi cikin kasar.
Akwai kuma tsoron kara farashin kiran waya na iya kara ta'azzarar lamura a tsakanin miliyoyi na yan kasar dake tunanin sauyi. Kokari na cigaba ko kuma kara fadawa cikin ruwa na talauci, duk da cewar dai masu mulkin tarayyar Najeriyar suna fadin an kare hawa, har yanzu babu alamun aikin manufofi na tattali na arzikin kasar.
Mahukuntan tarrayar Najeriya dai na a tsakanin burge yan kasar kafin zabe da kila ma fadawa rudanin da bashi da adadi a lokaci na hukunci na yan kasa.