1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Asarar rayuka a rikicin zabe

Abdul-raheem Hassan
February 25, 2019

Kungiyoyin fararen hula sun tabbatar da mutuwar kimanin mutane 39 a sassa daban-daban na Najeriya, wasu 128 kuma na hannun 'yan sanda bisa zarginsu da alaka da tayar da zaune tsaye yayin gudanar zabubbuka.

https://p.dw.com/p/3E1p2
Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Shugaba Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDPHoto: Atiku Media Office

Hukumar Zaben Najeriyar INEC dai, ta sanar da cewa za ta ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi bayan jinkirta karba daga matakin jihohi, sakamakon wasau matsaloli da tace sun sha kanta. Sai dai gabannin sanar da sakamakon a hukumance magoya bayan manyan 'yan takarar shugabancin kasar biyu na APC mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ta PDP, na ikirarin samun nasara.

A yanzu haka dai hankali ya fi karkata ne kan 'yan takarar jam'iyyun APC da PDP, inda shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da ke neman wa'adin shugabancin kasar karo na biyu ke karawa da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Tun da fari dai, hukumar ta INEC ta dage ranar da aka shirya gudanar da zabukan tun farko, sa'o'i kasa da biyar a fara zabukan, inda ta ce ta fuskanci wasu matsaloli da suka hada da rarraba wasu muhimman kayayyakin zaben cikin lokaci.