1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magance garkuwa da mutane a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 21, 2022

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, ta bayyana cewa rashin shugabanci ne ya jefa su cikin matsalolin da suke ciki a Najeriya a yanzu haka.

https://p.dw.com/p/47NSi
Najeriya Fulani-Nomaden
Ana dai alakanta garkuwa da mutane da Fulani, baya ga rikicinsu da manoma a kasarHoto: AFP/Luis Tato

Wannan ne mataki na farko da sabon shugaban kungiyar ya bayyana, bayan  murabus din da tsohon shugaban ya yi. Kokari ne dai na fadawa juna gaskiya a kan lalacewar al'ammura da kalubalen da Fulani makiyayan ke fuskanta a Tarayyar Najeriyar, inda matsalar 'yan bindigar daji ta haramta noma da kiwo a jihohi da dama na kasar. Tuni dai gwamnati ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda. Sakataren kungioyar ta Miyetti Allah Baba Usman Nganjarma ya bayyana matsalolin rashin tsaro na satar shanu da garkuwa da mutane, a matsayin abubuwan da ke tayar musu da hankali wanda tilas su nemi mafita.

Zanen barkwanci I Garkuwa da mutane a Najeriya
Masu garkuwa kan sace tare da tsare mutane domin neman kudin fansa

Alhaji Yusuf Hussani Bosso shi ne sabon shugaban riko na kungiyar ta Miyeeti Allah ta Macban, wacce ita ce babba kuma matattara ga mafi yawan Fulanin Najeriyar da ma wasu kasashen Afrika ta Yamma. Samun  sabon shugaba na rikon dai, ya sanya zura ido a kan abin da za su yi dangane da matsalar da ta addabi kowa. Ana cike da fata ta samun sauyi daga wadannan matsalolin na 'yan ta'addan daji da ta kai wa kowa iya wuya a Najeriyar, ban da rashin tsaro da tashin hankali na kashe-kashen mutane da ya janyo kasar ke fuskantar barazanar yunwa a yanzu.