1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLatin Amurka

Mexico za ta sami mace shugabar kasa

Abdullahi Tanko Bala
September 7, 2023

Mexico na shirin zabar mace shugabar kasa ta farko a tarihin kasar a zaben 2024 da za a gudanar. Jam'iyyar da ke mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa dukkaninsu sun tsayar da yan takara mata a zaben na 2024.

https://p.dw.com/p/4W4Z3
Bildkombo | Claudia Sheinbaum und
Hoto: Fernando Llano/Marco Ugarte/AP Photo/picture alliance

Jam'iyya mai mulki ta tsayar da wata wadda ta taba rike mukamin magajin garin birnin Mexico Claudia Sheinbaum a matsayin yar takararta a zaben da za a yi a ranar 2 ga watan Juni.

Sheinbaum dai tana da kusanci da shugaban kasar Andres Manuel Lopez Obrador wanda ba a amince ya sake tsayawa takara  ba bayan wa'aadin shekaru  shida a karagar mulkin

A makon da ya gabata kawancen Jam'iyyun adawa suka tsayar da Sanata kuma kwararriyar Inginiyar Kwamfuta Xochitl Galvez a matsayin wacce za ta yi musu takarar shugabar kasa.