1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jama'a sun hana sauke kayan zabe a Mexico

Ramatu Garba Baba
June 30, 2018

Shugabanin al'umomi sun sha alwashin hana jama'a kada kuri'a bisa abinda suka kira gazawar gwamnati a fannin inganta rayuwar al'umma yayin da ake shirin gudanar da babban zaben shugaban kasar ta Mexico a gobe Lahadi.

https://p.dw.com/p/30acd
Mexiko Wahlen Boykott
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Blackwell

Rahotannin sun nuna cewa jama'a na yaga fostar kamfain na 'yan takara dama wasu da suka kafa shingaye don hana jami'an hukumar zabe sauke kayyakin aikinsu. Tuni ma dai jami'an hukumar zaben suka baiyana wasu birane goma sha shida a matsayin yankunan da ke tattare da hadura bisa barazana da a ke fuskanta daga al'umma yankunan.

 Andres Manuel Lopez Obrador shi ne mutumin da ake ganin zai kawo sauyi a mulkin kasar muddun ya lashe zaben sai dai ya gagara samun hadin kan al'ummar da ke baiyana takaici kan yadda 'yan siyasa suka zabi su azurta kansu maimakon inganta rayuwar al'ummar da suka zabe su.