1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta sassauta dokar zaman gida

Abdourahamane Hassane LMJ
April 16, 2020

Gwmanatin Jamus ta ba da sanarwar yin sassauci a kan matakan da ta dauka domin dakile yaduwar annobar cutar Coronavirus, amma kuma tare da yin taka tsan-tsan na ci gaba da haramta cunkoson jama'a.

https://p.dw.com/p/3b1xG
Deutschland PK Merkel zur Corona-Pandemie
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Reuters/B. von Jutrczenka

Shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ce ta bayyana hakan, inda ta ce duk da nasarorin da suka cimma a yaki da annobar ta COVID-19 a cikin jihohin kasar 16, hakan ba zai sa su yi sake ba wajen kara jan damara. Merkel ta kara da cewa daga ranar hudu ga watan Mayu za a sake bude makarantun firamare da sakandare. Sai dai kuma sassaucin bai shafi yin tarurruka da suka hadar da na mawaka da na wasanin ba, inda haramcin yin irin wadannan tarurrruka zai ci gaba har zuwa karshen watan Augusta. 

A jawabin nata dai, Merkel ta ce shagunan da ke girmansu ya kai mita 80, za su iya sake budewa, amma tare da tsarin tsabta da kuma kaucewa dogayen layuka tana mai cewa:

Deutschland Corona-Pandemie | Hotspot Heinsberg | Rewe-Mitarbeiterin
Za a asake bude shaguna a JamusHoto: picture-alliance/dpa/J. Güttler

"Mun umarci jama'a da su rika saka takunkumin rufe fuska wanda ya dace a kullum musamman a cikin motocin haya da kuma cikin shaguna lokacin sayaya, hakan zai kareku tare da kare wasu."

Koma bayan tattalin arziki

Sai wadannan tarin matakai da gwamnatin ta dauka, sun janyowa kasar koma bayan tattalin arziki tun cikin watan Maris, kamar yadda ofishin ministan tattalin arikin Jamus din ya bayyana tare da yin gargadin cewar za a ci gaba da tafiya a haka har zuwa tsakiyar wannan shekarar. Daman dai tattalin arzikin Jamus da ke zaman kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai, ya yi rauni a shekarar da ta gabata sakamakon rikicin kasuwanci na duniya da aka yi ta fama da shi gabanin barkewar annobar ta Coronavirus ta kara saka kasar cikin matsalar tattalin arzikin.

BMW-Werk Leipzig
Kamfanonin kera motoci na kirga asaraHoto: picture-alliance/dpa/J. Woitas

Merkel dai ta ce za su duba su ga yadda matsalar ta Coronavirus take cikin kwanaki 14 domin sanin ko an samu sauki ko akasin haka, ta yadda za su gane cewar ko sassaucin da mahukuntan na Jamus suka yi ya kara janyo cutar. Merkel ta bayyana cewa za su fara sanya idanu daga ranar 20 ga wannan wata na Afrilu da muke ciki zuwa uku ga watan Mayu mai zuwa, kafin sanin matakin da ya kamata su dauka a gaba. 

Kamfanoni na kirga asara

Yanzu haka dai manyan kamfanon na kera motoci irin su Volswagen da Daimler sun rufe wani bangaren aikinsu. Wasu daga cikin wadannan kamfanonin dai ba su taba kirga asara irin wannan ba, cikin shekaru 30 din da suka gabata, inda rahotanni ke nunar da cewa suna yin asarar kusan kaso 37 cikin 100 na motocin da suke kerawa. Domin fuskantar wannan lamarin dai, gwamnatin ta Jamus ta bullo da wani tsari na biliyoyin daloli domin tallafawa kamfanoni. Kimanin kamfanonin dubu 725 ne dai za su samu wannan tallafin. Alkaluman da aka ba da zuwa yanzu game da cutar ta Coronaviru a Jamus, ya nunar da cewa mutane sama da dubu 120 ne ke fama da cutar ta COVID-19, yayin da kimanin 3,254 suka mutu.