1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Me goyon bayan Israila ke nufi ga Amurka?

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2024

A yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara yin kamari, Amurka ta ci gaba da yin tsayuwar da a goyon bayan da ta ke nuna wa Israila. Kwararru na cewa Amurka na ma iya tallafa wa Israila a rikicinta da Iran.

https://p.dw.com/p/4lQAp
Dangantakar Amurka da Israila, Joe Biden da Benjamin Netanjahu
Dangantakar Amurka da Israila, Joe Biden da Benjamin Netanjahu Hoto: Miriam Alster/UPI Photo/imago images

Amurka ta jaddada goyon bayanta ga babbar aminiyarta Isra'ila a yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara zafafa, al'amura kuma ke kara kara tabarbarewa. Shugaba Joe Biden na Amurka ya nanata kudurinsa na ci gaba da agaza wa Isra'ila ta ko wane hali, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, yayin ganawa da jagororin kungiyar kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya wato G7.

Furucin jadda goyon bayan Biden na zuwa ne a daidai lokacin da yankin Gabas ta Tsakiyake kan tsini tun bayan harin da mayakan Hamas suka kai a kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023, harin da ya kashe kusan mutum 1,200 tare da garkuwa da wasu 250, inda har yanzu ake tsare da wasu a Gaza.

Karin Bayani:Yaushe za a tsagaita wuta a Gaza?

Shugaba Biden da Benjamin Netanyahu a 2023
Shugaba Biden da Benjamin Netanyahu a 2023Hoto: Evelyn Hockstein/File Photo/REUTERS

A wani mataki na ramuwar gayya, Isra'ila ta kaddamar da wani gagarumin farmakin soji a yankin Falasdinu, wanda manufarsa ita ce shafe Hamas da kuma kubutar da mutanen da ta yi garkuwa da su. Tun daga farkon wannan farmakin, an kashe mutane fiye da 40,000 a Gaza, yawancinsu fararen hula.

Bugu da kari ana kara gwabza fada tsakanin sojojin Isra'ila da kungiyar Hizbullah, kawancen Hamas da ke kasar Lebanon da ke harba makamai masu linzami kan Isra'ila daga kan iyakar arewacin kasar da Lebanon. A ranar Litinin din da ta gabata ce Isra'ila ta kaddamar da farmaki ta kasa kan Lebanon, bayan da ta kashe shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah

Karin Bayani:Fargabar ta'azzarar rikici bayan kisan Nasrallah

Amurka ta yi amfani da matsayinta na babbar kawar Isra'ila don yin kokarin tasiri a kanta don ba da damar karin taimako a Gaza. Amma kamar yadda Biden ya sake tabbatarwa, goyon bayan Washington ga Isra'ila zai ci gaba. Sai dai hakan ba yana nufin cewa shugabannin kasashen a kodayaushe suna samun jituwa ba ne. Jonathan Panikoff darakta ne a cibiyar tsaro ta Gabas ta Tsakiya ta Scowcroft..

Joe Biden a lokacin da ya kai ziyara Israila
Joe Biden a lokacin da ya kai ziyara IsrailaHoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

"Yana da muhimmanci a bambanta dangantakar Shugaba Biden da kasar Isra'ila da kuma ta firaminista Netanyahu. Ya shafe shekaru da dama yana alaka mai tangal tangal da Netanyahu. Amma babu abun da ya taba sadaukarwar Biden ga Isra'ila da tsaron Isra'ilar. "

Jami'an Amurka sun jaddada cewa suna son kauce wa yakin da ake yi a yankin da kuma cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, domin a sako mutanen da aka yi garkuwa da su. Sai dai a ranar Talata Iran ta harba makami mai linzami kan Isra'ila, lamarin da ke nuni da ta'azzarar rikicin a maimakon samun mafita.

Karin Bayani:Iran ta kai wa Isra'ila hare-hare 300 da jirage marasa matuka

Ana iya ganin misali daya na irin dangantakar da ke tsakanin gwamnatin Biden da Isra'ila ta hanyar yanke shawarar da Isra'ila ta yi na kashe Hassan Nasrallah ba tare da neman shawarar Amurka ba a cewar William Wechsler Babban Darakta a Cibiyar Rafik Hariri da ke nazarin harkokin Gabas ta Tsakiya a Washinton.

Karin Bayani: Hezbollah ta tabbatar da kashe Hassan Nasrallah

Netanjahu da Biden a birnin Kudus a 2010
Netanjahu da Biden a birnin Kudus a 2010Hoto: AP

"Babu wani aminci ko yarda tsakanin Biden da Netanyahu. Makon da ya gabata, Amurka ta maida hankali kan kokarin cimma shawarwarin tsagaita wuta na kwanaki 21 a kan iyakar Isra'ila da Lebanon. A yayin da suke tattaunawa da Isra'ilawa, a daya hannun 'yan Isra'ila suna shirin kashe Nasrallah kuma ba su gaya wa gwamnatin Biden shirinsu ba, an sami raguwar aminci sosai tsakanin bangarorin biyu."

Yayin da al'amuran cikin gida ke taka rawa ga mafi yawan masu kada kuri'a, goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra'ila zai iya yin tasiri a zaben shugaban kasar Amurka mai zuwa. Wasu Amurkawa sun nuna rashin jin dadinsu a game da rawar da Washinton ke takawa a rikicin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda ake iya gani a zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa da ta bazu a harabar jami'o'i a fadin Amurka a lokacin bazarar da ta gabata.