1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yaki ka iya mamaye Gabas ta Tsakiya - Scholz

September 26, 2024

Gargadin da shugaba Scholz ya yi, ya biyo bayan watsi ne da Isra'ila ta yi na tsagaita wuta a yaki da Hezbollah.

https://p.dw.com/p/4l7u4
Olaf Scholz da Benny Gantz
Olaf Scholz da Benny GantzHoto: Kugler, Steffen/BPA/dts Nachrichtenagentur/IMAGO

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi gargadi a ranar Alhamis cewa yakin da Isra'ila ke yi da Hezbollah ta Lebanon ka iya fantsama yankin Gabas ta Tsakiya gaba daya.

Mista Scholz ya yi gargadin ne bayan tattaunawa da dan siyasar Isra'ila na bangaren adawa Benny Gantz.

Gantz ya kasance tsohon kwamandan sojin Isra'ila kuma daya daga cikin mambobin majalisar zartar da harkokin yaki ta Netanyahu wanda ya ajiye aikinsa a watan Yuni bayan ikirarin cewa babu tartibin tsari ga Gaza bayan yaki.

Karin bayani: Matsayar Jamus a rikicin Isra'ila da Hamas

A yayin ziyarar tasa a Berlin, Gantz ya kuma gana da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier  da kuma wasu kusoshin kasar domin tattauna yakin da kasarsa ke yi da Hamas a Gaza da kuma Hezbollah a Lebanon.

Karin bayani: Faransa da Jamus da Burtaniya na son a dakatar da yakin Gaza

Jamus ta bi sahun wasu kasashe da suka yi gamayya daya domin kiran a tsagaita wuta na kwanaki 21 a yakin da Isra'ila ke tafkawa da Hezbollah.