1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD ta yi Allah-wadai da kisan 'yar gudun fanfalakin Yuganda

September 5, 2024

Hukumomi sun ce ana zargin tsohon saurayinta ne ya cinna mata wuta, sannan ta mutu sakamakon raunuka da ta samu.

https://p.dw.com/p/4kKXw
'Yar gudun fanfalaki Rebecca Cheptegei
'Yar gudun fanfalaki Rebecca CheptegeiHoto: Chai v.d. Laage/IMAGO

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kisan  'yar gudun fanfalaki ta Yuganda Rebecca Cheptegei.

Mai magana da yawun majalisar Stéphane Dujarric ya fada a ranar Alhamis cewa dole ne a dauki mataki kan wanda ya haddasa mutuwar 'yar wasan.

MDD ta damu a game da sabbin dokokin da'a a Afganistan

Rabecca ta mutu ne sakamakon raunuka da ta samu daga kunar wuta da ake zargin tsohon saurayinta ne ya zuba mata fetur ya kona ta, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Lebanon: MDD ta tsawaita wa'adin rundunar UNIFIL

'Yar gudun fanfalakin mai shekara 33, wacce ta halarci gasar guje-guje da tsalle-tsalle na 2024 da ya gudana a birnin Paris na Faransa, ta kone sosai a duk jikinta, lamarin da ya haddasa mutuwar ta.