1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi gargadi kan baraznar yunwa a arewacin Najeriya

June 29, 2024

Wata kungiyar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce har yanzu tana kokarin samo kudaden yaki da tsananin karancin abinci a jihohi uku da rikicin Boko Haram ya shafa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4heua
Guda daga cikin dubban yara da ke fama da matsalar rashin abinci a arewacin Najeriya
Guda daga cikin dubban kananan yara da ke fama da matsalar rashin abinci a jihar Borno.Hoto: Adam Abu-bashal/AA/picture alliance

Shugaban kungiyar agaji ta OCHA, Mohamed Malick Fall ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa har yanzu kasashen da suka yi alkawarin bayar da tallafin kudade a baya, ba su cika alkawuran da suka dauka ba.

Cikin watan Afrilun ne kungiyar ta kaddamar da gangamin neman dala miliyan 306 tare da gwmanatin Najeriya, a madadin mutum miliyan biyu da dubu 800 wadanda ke fama da barazanar yunwa a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.

Sai dai jami'in ya amince cewa matsalolin tattalin arziki da annobar corona ta haddasa, na iya zama dalilain rashin cika alkawuran da suke kokawa a kai.

Kungiyar ta agaji wato OCHA, ta kuma yi gargadi da abin da ta kira bala'i da za a iya gani daga karancin abinci a arewa maso gabashin Najeriyar, muddin aka gaza kawo dauki cikin lokaci.