1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta nanata kiran tsagaita wuta a Gaza

Abdullahi Tanko Bala
January 17, 2024

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce bangarorin da ke yaki a Gaza suna keta dokokin kasa da kasa ya kuma bukaci su aiwatar da shirin tsagaita wuta nan take

https://p.dw.com/p/4bNRB
Schweiz | Weltwirtschaftsforum 2024 Davos
Hoto: Gian Ehrenzeller/KEYSTONE/picture alliance

Da yake magana a taron tattalin arzikin duniya a Davos, Guterres ya ce bangarorin biyu da ke yaki sun saba dokokin kasa da kasa da aka cimma na Geneva da ma kuma kudirorin Majalisar Dinkin Duniya.

Ya ce duniya ta zuba ido ta na kallo ana kashe fararen hula yawancinsu mata da kananan yara, ana yi musu luguden bama bamai da tilas ta musu barin gidajensu da kuma hana musu damar samun taimakon jin kai.

Karin Bayani: Yunkurin dakatar da yakin Gaza

"Ya ce ina kara nanata kiran tsagaita wuta nan ta ke don taimakon jin kai da shirin da zai kai ga samun zaman lafiya mai dorewa tsakanin Israila da Falasdinawa bisa masalahar kasashe biyu da za su zauna daura da juna cikin lumana da kwanciyar hankali. Wannan ita ce kadai hanyar da za a kawo karshen wahalar da jama'a suke sha da kuma hana yaduwar rikicin a yankin baki daya "

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita wuta yana mai cewa Israila za ta ci gaba da kai farmaki a Gaza har sai ta ga bayan Hamas ta kuma kwato mutanen da Hamas din ta yi garkuwa da su a ranar  7 ga watan Oktoba.