1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD ta bukaci yin binciken gaggawa a kan hare-haren Filato

Zainab Mohammed Abubakar
December 28, 2023

Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya firgita matuka sakamakon hare-haren da aka kai wa kauyukan tsakiyar Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 200.

https://p.dw.com/p/4afss
Volker TürkHoto: Salvatore Di Nolfi/REUTERS

A cikin wata sanarwa Volker Turk  ya bukaci mahukuntan Najeriyada su kafa hukuma mai zaman kanta da za ta gudanar da binciken harin cikin gaggawa, daidai da dokokin kare hakkin bil'adama a duniya, tare da hukunta wadanda ke da hannu.

Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun kaddamar da hare-hare tsakanin yammacin ranar Asabar zuwa safiyar Talata a jihar Filato, yankin da ya shafe shekaru da dama yana fama da rikicin addini da na kabilanci.

Yankunan Arewa maso Yamma da tsakiyar Najeriya sun dade suna fama da matsalar ta'addancina 'yan bindiga da ke kai hare-hare a kan kauyuka domin yin fashi da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.