Mawakiya bayan kaura: Nneka daga Najeriya
Mawakiyar Hip-Hop da Soul, Nneka Egbuna ta sha kai komo tsakanin nahiyoyi biyu: Kasarta ta asali Najeriya da Jamus. Ta rera wakoki kan wannan batu da na rigingimu da kuma na gurbatar muhalli a Afirka.
Kaura, 'Yanci, Nasara
Lokacin da Nneka ta zo birnin Hamburg a karshen shekarun 1990, Jamus ta kasance kasa mai cike da zaman lafiya da 'yancin da ba ta taba gani ba. Amma ta yi fama da wariyar fata, an kirata "Nigger". Ta hadu da ire-irenta a fagen kida. A 2004 likafarta ta yi gaba lokacin da ta yi wakar share fage a bikin wakoki na dan Jamaica Sean Paul a dandalin Stadtpark da ke Hamburg.
Najeriya kasa mai fama da rikice-rikice
An haifi Nneka Egbuna a garin Warri a 1980. Garin da ke a jihar Delta daya daga cikin jihohin Niger Delta mai arzikin man fetur, yana da yawan mutane fiye da dubu 500. Kabilun Ijaw, da Itsekiri da kuma Urhobo ke da rinjaye a jihar. Ana yawan samun rikicin kabilanci a garin na Warri.
Dinbin mai - kudi kadan
Alal misali kabilu daban-daban na takaddama game da shugabancin aikin hakar mai. Najeriya ce ta 10 a kasashe masu arzikin mai a duniya, ita ce ta daya a nahiyar Afirka: Man na sama mata kashi 70 cikin 100 na kasafin kudinta. Sai dai a Niger Delta ba a ganin tasirin wannan arziki. Maimakonsa ma gurbatar muhalli ke barazana ga rayuwar mutane da dabbobi.
Wakokin tir da ta'addanci
Rashin adalci da cin hanci da rashawa a kasar sun janyo matsaloli musamman bullar kungiyar Boko Haram a arewacin kasar. A rubuce-rubucenta kan siyasa da zamantakewa Nneka na tabo batun: A wakarta mai taken "Pray For You" ta yi tir da kisan da kungiyar ta yi wa Kiristoci. A wannan hoto mata ne da ke makokin 'yan uwansu da aka kashe a wani harin kunar bakin wake da Boko Haram ta kai.
"Ku farka, Afirka!"
Fice da Nneka ta yi a duniya yana taimakawa wajen bayyana halin da Najeriya ke ciki. Tana waka kan kamfanonin duniya masu samun kazamar riba amma jama'a ba ta gani a kasa, kamar yadda mai ya bata dangantaka. Tana kuma kira ga Afirka da ta dauki nauyin kanta, ta daina neman dora laifi kan tsoffin 'yan mulkin mallaka - kamar a cikin wakarta mai taken "Africans".
Nneka: "So duka so ne, amma son kai ya fi."
Ba korafe-korafen siyasa da zamantakewa suka mamaye wakokinta ba. Tana nanata muhimmancin kyakkyawar tarbiyya da iyali a wakokinta. Kamar yadda take fama da matsala a matsayin Bajamushiya 'yar Afirka da banbancin al'adu guda biyu. Sai dai ta samu matsaya tsakkanin sassan biyu: "Muhimmin abu shi ne ka so kanka."