1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin kasashen Afirka a rikicin Rasha da Ukraine

Abdourahamane Hassane M. Ahiwa
April 21, 2022

Afirka ta rabu a kan batun daukar bangare a yakin da ke faruwa a Ukraine, inda kasashen biyu masu rikici ke kokarin samun kuri'un kasahen na Afirka ta kowane yanayi.

https://p.dw.com/p/4AExR
Äthiopien | AU Gipfel in Addis Abeba | Mohammed Schtajjeh
Hoto: Shadi Hatem/APA Images/ZUMAPRESS/picture alliance

A farkon mamayar Rasha a Ukraine a cikin watan Fabrairun da ya gabata, yawancin kasashen Afirka suna yi wa wannan rikicin kallo a matsayin wani yakin da ya yi nisa da su sossai. Amma a farkon watan Maris, lokacin da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a kan wani kudiri na neman Rasha ta daina amfani da karfi a kan Ukraine, kasashen Afirkar wasu sun kada kuriar wasu kuma suka kaurace wasu kuma sun ki amincewa.

Kasashen Afirka 10 ne suka kada kuri'ar amincewa, 9 suka ki, a yayin da 24 suka kaurace, sannan goma sha daya ba su shiga zaben ba. Alkaluman wannan kuri'a ta biyu sun shaida irin abin kunyar da nahiyar ke fuskanta a yakin da bai shafe ta ba da kuma inda take da hatsarin daukar bangare.

Ana dai tunkarar su da hujjoji mabanbanta. Ukraine takan ce 'muna fuskantar zalunci na yan mulkin mallaka, ku da kanku kun san mene ne mulkin mallaka. Rasha ana ta bangaran takan ce ba mu taba samun tarihin mulkin mallaka ba  a Afrika, mun goyi bayan yunkurin 'yantar da ku a gwagwarmaya da ku yi.

Ukraine-Krieg - Präsident Selenskyj
Shugaba Volodymyr Zelenskyy na UkraineHoto: Ukrainian Presidential Press Office/AP/dpa/picture alliance

A halin yanzu, Ukraine na kokarin shawo kan kungiyar Tarayyar Afirka gaba daya don bai wa shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy damar yin magana a cikin wannan kungiyar, kamar yadda ya yi a majalisun dokoki na kasahe dabam-dabam na duniya.

Irin wannan tataunawar dai tana kan batutuwan da za a tattauna a kasar Kenya, wadda a halin yanzu ta kasance memba na dindindin a kwamitin sulhu na MDD, domin jakadan Ukraine dake a Nairobi ya gabatar da jawabinsa ga majalisun biyu.

Sai dai ita ma Rashar tana cin gajiyar gagarumin tallafin da take bayer wa a nahiyar Afirka misali a Mali da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya inda take da sojoji, takan yi fafutuka a shafukan sada zumunta da kafofin yada labarai na nuna kusancinta da Afrika saboda abinda ta kira rashin cin zalun da ba ta yi ba a nahiyar na mulkin mallaka.