1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yawan jama'a, yawan matsaloli

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 6, 2023

Hukumar Kidayar Jama'a ta Najeriya ta bayyana cewa a hasashenta yawan al'ummar kasar ya kai miliyan 216, a daidai lokacin da take shirye-shiryen gudanar da kidayar jama'ar domin tantance adadinsu.

https://p.dw.com/p/4TXAk
Najeriya | Kidayar Jama'a | Al'umma | Matasa
Yawan al'umma ka iya haifar da tarin matsaloliHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

Kiyasta yawan al'ummar da Najeriyar ke da su a kan wannan adadi na mutane miliyan 216 dai, ya nuna kasar zama cikin jerin kasashen da suka fi samun karuwar jama'a a duniya. Hakan dai na nufin al'ummar Najeriyar, na karuwa da sama da kaso uku cikin 100 a kowace shekara. Kiyasin da kuma ya yi hasashen cewa fiye da kaso 60 cikin 100 na al'ummar Najeriyar matasa ne masu jini a jika, na nunar da cewa kamata ya yi ya zama abin alfahari ga kasar ganin cewa yawan al'umma abu ne mai kyau ga kasa kamar Najeriyar sai dai abin ba haka yake ba. Samun dandazon matasa masu jini a jika ga kowace al'umma na da muhimmanci ga ci-gaban kasa, amma rashin amfani da hakan na zama kaulabale mai yawan gaske ga kasar.

Najeriya | Kidayar Jama'a | Al'umma | Matasa | Mata | Yara Kanana
Mata da kanan yara ne suka fi fuskantar kalubale, sakamakon yawan al'umma Hoto: Getty Images/AFP/O. Omirin

Shekaru 16 kenan dai rabon da Najeriyar ta gudanar da kidayar al'ummarta, abin da ya sanya masana ke bayyana hasashen zahirin yawan al'ummar kasar da cewa akwai hadari tattare da shi. Wani abu dangane da batun yawan alumma a Najeriya dai shi ne, lamari ne da ke cike da tunani na siyasa da addini da ma tattalin arziki. A yayin da gwamnati ke kallon yawan jama'ar a matsayin batu da zai taimaka wajen yin tsare-tsare domin samun ci-gaban kasa, amma akasin haka ke faruwa. A yanzu dai Hukumar Kidayar Jama'ar ta Najeriya ta kammala shirin sake kidaya 'yan Najeriyar, domin sanin adadinsu bayan dakatar da aikin da tsohuwar gwamnatin kasar ta yi. Kafin wannan lokaci kuma za a ci gaba da aiki da hasashen na yanzu a  Najeriyar, kasar da ke kan gaba wajen yawan al'umma a nahiyara Afrika.