1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yawan masu zaman kashe wando ya karu

Uwais Abubakar Idris AMA
March 16, 2021

'Yan Najeriya na mayar da martani kan rahoton hukumar kididigar jama'a, da ya nuna cewa yawan marasa aikin yi ya karu zuwa kashi 33.3 cikin dari a tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/3qhUD
Nigeria Maßnahmen gegen die Wüstenbildung
Hoto: DW/Thomas Mösch

'Yan Najeriya kaso 33.3 cikin dari ne ke fama da rashin aikin yi, wanda wannan shi ne kaso mafi muni na yawan mutane miliyan 23 da basu da aiki, wanda ya hakan ya kara fito da koma bayan tattalin arzikin da Najeriyar ke ciki a yanzu a zahiri.

Karuwar yawan mutanen da ke zaman kashe wando ba don suna so ba bisa yanayin da kasa ta samu kanta, na kara nuna hali na talauci da 'yan Najeriya suka fada, duk kasancewarta daya daga kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, kuma ta kan gaba da yawan jama'a a nahiyar. Alkaluma nuna cewa ‘yan Najeriya milyan 98 ne ke cikin hali na talauci daga adadin mutane miliyan 200 da kasar ta ke da su.

Karin Bayani: CBN ba ya ki maida hankali kan 'yan Arewa

Irin halin da Najeriyar ta ke ciki na kalubalen rashin tsaro kama daga matsalar ta'adanci zuwa ga rigingimun manoma da makiyaya da masu garkuwa da jama'a, an dade ana danganta su da matsalatr rashin aikin yi a tsakanin al'umar ta Najeriyar, kuma masanan Najeriya irinsu Dr Yahuza Getso na ganin cewar hakan yayi mumunan illa ga rayuwar jama'a, wanda ya ce "Dole ne a tashi haikan don magance matsalar rashin aikin yi ga mutane, da inganta fannin ilimi, idan ana fatan ganin samun sauki cikin gagawa."

Karin Bayani: 'Yan kasa na cikin kuncin rayuwa a Najeriya

Bukatar sauyi ga daukacin yanayin da Najeriya ta samu kanta ba zai ta'allaka kawai ga batun rashin ilimi kadai ba, akwai har da rashin ingantaccen ilimin da kwarewar aiki lamarin da ke barazana ga batun tsaro. Tun daga 2016 Najeriya ke samun karuwar marasa aikin yi bisa karayar tattalin arzikinta, wanda ya kuma fannoni da dama cikin matsala da koma baya, duk da yake gwamnatin dama ta yi hasashen faruwarsa in har ba'a dauki matakin da ya dace ba.