1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HdM: Matashiya mai sana'ar zane

March 23, 2021

A jihar Katsina da ke Najeriya, wata matashiya ta kama sana'ar zana fulawoyi da tsaunika da ruwa kuma rubutun larabci domin kwalliyar gidaje da ofisoshi, a wani mataki na dogaro da kanta.

https://p.dw.com/p/3r0pE
Schnitzerei und Kalligraphie Zentrum in Kabul
Matashiya mai sana'ar zane a KatsinaHoto: DW

Wannan Matashiya mai suna Hauwa'u Lawal tana gudanar da wanann sana'ar ne a gidan mahaifinta da ke cikin birnin Katsina, kuma ta ce ta koyi sana'ar ne ta hanyar kallan talabijin, hakan ya sanya mata ra'ayin ci gaba yin zanen a matsayin sana'a. Matashiyar ta ce ta samu nasarori sosai da sanar, inda take kai zanan zuwa Kaduna da Kano da Abuja tana sayarwa.

Hauwa'u ta ce daga cikin nasarar da ta samu yanzu, ta zama cikakkar ma dogaro da kanta, koda yake ba a rasa kalubale. Ganin muhammancin sana'ar da alfanunta, yasa Hauwa'u ta zaburar da 'yan uwanta mata kan cewa su tashi su kama sana'a domin su tsira da mutuncinsu. Hauwa'u dai na da yayu maza da ke taimaka mata wajan gudanar da wannan sana'a, domin ta cimma burinta.