1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai kafar jarida ta yanar gizo

June 23, 2021

A kokarinsa na samun dogaro da kai da kuma taimakawa 'yan uwansa matasa, wani matashi da ya kammala karatun sakadndare ya bude kafar jarida ta yanar gizo.

https://p.dw.com/p/3vQeU
Wani matashi a Lagos da ke nazari ta yanar gizo
Wani matashi a Lagos da ke nazari ta yanar gizoHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Abubakar Shafi'i Alolo Matashi ne a jihar Katsina da ya kammala karatun sakandare ya bude kafar jarida ta yanar gizo inda ya dauki matasa kusan 20 aiki.

Daga cikin matasan akwai masu digiri da masu Diploma da kum NCE. Jaridar dai ya sanya mata suna "Mobile Media Crew" a turance.

Ya rarraba matasan aiki a matsayin wakilai a fadin jihar wadanda ke dauko masa rahotanni. Wasu kuma na zaune a ofishin da ya bude inda ya zuba komfutoci. 

Matashi shafi'i yace ya samu nasarori sosai tun daga kafa wannan jarida ta yanar gizo kawo yanzu.

Matashin dai yace yana samun kudaden shiga ta hanyar hotuna da video da yake dorawa a shafikansa.