1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramta zanga-zanga a Lagos

Abdourahamane Hassane
February 11, 2021

Hukumomi a Najeriya sun yi kashedi ga masu aniyar yin gangami a ranar Asabar a birnin Lagos domin neman shari'a ta yi aikinta bayan cin zarafin da aka yi wa matasa.

https://p.dw.com/p/3pF7H
Nigeria Lagos | Protest EndSARS
Hoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture-alliance

Watannni hudu bayan zanga-zangar ta EndSARS da aka yi a birane da dama na Najeria da nufin kawo karshen aikin rundunar ta musammun ta 'yan sanda mai yaki da 'yan fashi da makami saboda ta'adin da ta yi wa al'umma. Shugabannin tsara zanga-zangar sun ce har yanzu babu wani daga cikin jami'an tsaron da aka hukunta wadanda suka bude wuta da harsashen gaske a kan fararan hula suka kashe rayuka. Tashin hankali da ya afku a ranar 20 ga watan Oktoban da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta ce jami'an tsaro 43 suka mutu yayin da farar hula 57 suka kwanta dama.