1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan magance rikicin makiyaya da manoma

Uwais Abubakar Idris
January 8, 2018

Gwamnatin Najeriya za ta girke jami’an tsaro da za su kare gonaki da dabbobin domin kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.

https://p.dw.com/p/2qXFu
Nigeria Konflikt Farmer Pastoralisten
Hoto: DW/K. Gänsler

Manyan jami'an kula da harkokin tsaro a karkashin ministan kula da harkokin cikin gida na Najeriyar sun gudanar da taro a Abuja, kan matsalar makiyaya da manoma. Ministan kula da ayyukan gona ya bayyana takaici kan yadda aka kashe jama'a a rikicin makiyaya da manoma a jihar Benue, abin da ke haifar da Karin fuskantar zaman tankiya a jihar da ma wadanda ke makwabtaka da ita.

Lamarin da ministan ya ce baya ga asarar rayuka, tana barazana ga afkuwar 'yunwa domin kuwa manoman ba za su iya gudanar da aikinsu ba, su kuma makiyaya na cikin tasku. Wannan ya sa gwamnonin jihohin Benue da Nasarawa da Taraba da Kaduna da kuma Niger suka yi taro. Ministan kula da aikin gona na Najeriyar Audu Ogbeh ya bayyana  matakan da zasu dauka.

Nigeria Unruhen und Landwirtschaft
Hoto: AFP/Getty Images

"Babu abin takiaci da ya wuce irin wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa, amma  in zamu fada wa kanmu gaskiya shekaru 50 da suka gabata ba mu yi wa makiyaya wani tanadi kamar yadda muka yi wa manoma ba.''

A small farm of maize
Hoto: DW

A cewar ministan ana amfani da tsarin a kasar Habasha da ma sauran wasu kasashe, wanda kuma ya samu nasara. Minstan kula da harkokin cikin gida na Najeriya Janar AbdulRahman Dambazau ya bayyana cewa gwamnati ba za ta sa ido tana ganin masu mumunan aniya na ci gaba da karkashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Munin da wannan rikici na Benue ya yi, ya daga hankalin mahukuntan Najeriya da ya sanya ci gaba da tarba-tarba na dakile sake afkuwarsa, ko kuwa bazuwar lamarin.