1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata na shiga gararin aikatau a kasashen larabawa

Nasir Salisu Zango
September 26, 2019

Da yawa daga cikin irin wadannan mutane kan tsinci kansu a halin tsaka mai wuya inda suke fadawa garari a kasashen da aka kaisu domin neman arziki a karshe su kan gwammace komawa gida.

https://p.dw.com/p/3QJLE
Äthiopische Hausfrauen in Saudiarabien und VAE
Hoto: DW/S. Shibru

Hangen Dala Bahaushe yace ba shiga birni ba, da yawa mutane kan fuskanci yankan kunkurun Bala, a lokacin da suka gwammace yin kaura daga kasashensu a nahiyar Afrika domin shiga turai ko kasashen Larabawa inda suke tunanin da zarar sun je shikenan kakarsu ta yanke saka.

A yankin arewacin Nigeria yawanci su kan shiga yankin larabawa ne irinsu Dubai da Saudiyya ko kuma Oman da nufin neman arziki sakamakon rashin ingancin shugabanci a kasashen ‘yan rabbana ka wadata mu wanda masana suka ce shine ummul abaisin firgita alumma har ta kai suna barin gida domin tafiya kasashen waje. Harira Umar ta shiga irin wannan hali inda ta tafi kasar Oman amma a karshe ta dawo dutse a hannun riga.

Aisha Umar ita ce shugbar kungiyar wayar da kan mata da ake yiwa lakabi da hasken alumma, ta ce a ziyarar kwanannan da ta kai Saudiyya ta zanta da wasu mata da suke da na sanin shiga kasar domin aikatau.

Wasu daga cikin masu shirya tafiye tafiye kan yi amfani da zalamar tafiya wadannan kasashe da mutane ke yi inda suke karbe musu kudi suna yi musu wala-wala.

Sarkin Hausawa mazauna Dubai Alhaji Garba Garo daya daga cikin kasashen da ake mararin zuwa ya bayyana cewa mutane suna shiga ragaita basu ga tsuntsu basu ga tarko.

Yanzu haka dai akwai dumbin mutane da ke kukan cewar an kaisu ana azabtar dasu, wasu kuma na kukan cewar ‘yan uwnasu sun tafi babu labari sai dai kuma babu wata alama ta daukar mataki na kawo karshen wannan matsala.