1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tallafi ga masu kananan sana'o'i

Uwais Abubakar Idris AMA
September 18, 2020

Gwamnatin Najeriya ta bullo sabon shirin talafawa masu karamin karfi da suka fuskanci matsalar koma bayan tattalin arziki dalilin annobar COVID-19.

https://p.dw.com/p/3ihF9
Nigeria - Abuja tomato market
Hoto: DW/S.Olukoya

Wannan sabon shiri da aka tsara shi ta yadda za’a talafawa masu karamin karfi a Najeriyar ta hanyar basu talafi na ‘yan kudadde kyauta zuwa asusun ajiyarsu, kama daga masu tuyan kosai ko awara da masu tuka keke Napep da masu gyaran mota har da weadanda ke da kanana da matsakaitan masana’antu a Najeriyar za’a basu ‘yan kudadde don tallafa masu na tsawon watani uku. 

Duk da kyawon wannan tsari a rubuce da zai hada da malaman makaranta na firamare da sakandire da matsalar ta sanya rage masu albashi, amma ba a nan gizo ke sakarsa ba, domin a lokutan baya an sha koken ‘yan siyasa su mamaye lamarin inda akan bar wasu sassa a baya saboda matsala ta amfani da yanar gizio wajen rijista. 

Sai dai gwamnatin Najeriya tace bisa tsarin da ta yi ba za’a samun wannan matsala ba don sai an tabbatar da raba dai dai da kamanta adalci koda a yankunan da basu da yanar gizo, an tsara a ranar 21 ga watan nan za’a bude shafin yanar gizo na www.survivalfund.org don masu sana’oi su yi rijista inda har akwai tsarin sayen kayayyakin da suke samarwa irin su kyallen rufe baki da hanci da sinarin kasha kwayoyin cuta da ake shafawa a hannu.