1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta haramta shigar da masara

July 14, 2020

A wani abun da ke zaman ci gaba a cikin sabon tsari na ci da kai da ke zaman sabon kwazo, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da shigo da masara cikin kasar domin amfanin kowa.

https://p.dw.com/p/3fKA9
eco@africa Uganda Mais
Za a daina shigar da masara Najeriya, bayan an hana shigar da shinkafaHoto: DW

Babbar dabarar haramta shigar da shinkafa cikin kasar dai, ta yi nasarar samar da shinkafar mai tarin yawa domin ci da kai na miliyoyin al'umma ta kasar. Tsarin kuma da gwamnatin kasar ke neman kara tsawonsa zuwa masara, tare da kaddamar da wani sabon shirin haramta shigar da masarar da babban bankin kasar ya sanar.

Babu dala ga 'yan kasuwa

Kuma tun daga makon gobe ne dai, bankin ya ce ya tsayar da bayar da dalar Amirka ga masu son sayo masara ta waje, ko dai da nufin sarrafa ta wajen abincin kaji ko kuma ragowar bukatu na yau da na gobe. Abujar da ke cikin rashin kudi a halin yanzu dai, na fatan sabon tsarin na iya kai wa ga karshen asarar dubban miliyoyin daloli wajen sayo masarar daga manyan kasashe na duniya domin amfaninta.

Nigeria Reis-Produktion
Najeriya na kan gaba a noman shinkafaHoto: Imago Images/photothek/T. Imo

Abubakar Ali dai na zaman  masanin tattalin arzikin Najeriyar, da kuma ya ce shirin na iya taimakawa kokarin kasar na ci da kai dama wadatar da kai da abincin da ya taimaka mata a cikin kulle na coronavirus. Duk da cewar dai yawan masarar da Najeriyar take saye a waje ya ragu daga tan miliyan 700 a shekarar 2012 ya zuwa tan miliyan 400 a shekarar da ta shude, daga dukkan alamu manoman Najeriyar na da jan aikin cike gibin da ya kai kusan kaso 90 cikin 100 na tan miliyan 20 da kasar ta noma a shekarar da ta shuden.

Talaka cikin tasku

To sai dai kuma a fadar Bello Abubakar da ke zaman shugaban kungiyar manoman masara ta kasar, sun shirya tsaf da nufin fuskantar kalubalen mai girma. Cikin tsawon kasa da watanni guda uku dai, farashin masarar ya ninka da sama da kashi 100 a Najeriyar, a wani abun da ke zaman alamun girma na bukatar hajjar, farashin kuma da ke shirin ya karu sakamakon manufar haramta sayo masarar ta waje.