1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kin karbar 'yan gudun hijira Gaza a Masar

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 18, 2023

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce kasarsa ba za ta amince da kwararar 'yan gudun hijira daga yankin Zirin Gaza ba.

https://p.dw.com/p/4XhDl
Masar | Abdel Fattah al-Sisi | Jamus | Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-SisiHoto: Michael Kappeler/dpa/picrture alliance

Shugaban kasar Masar din Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana hakan ne bayan tattaunawarsa da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ke ziyara a Masar din, inda ya ce hakan zai bayar da kofar tilasta Falasdinawan da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan su fice zuwa Jordan din. Al-Sisi ya kuma dora alhakin gaza kai kayan agaji zuwa yankin Zirin Gaza da ke da mutane kimanin miliyan biyu da dubu 400, ga hare-haren da jiragen yakin Isra'ila ke kai wa mashigar Rafah da ta hada iyakar Masar da yankin na Zirin Gaza.