1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makwabtan Najeriya na kokawa kan rufe iyakoki

November 1, 2019

Cigaba da rufe iyakokin Najeriya na kara sanya mutanen da ke makwabtaka da iyakokin kasar bayyana irin yadda yanayin rayuwa ya kasance masu, misali garin Illela na jihar Sakkwato mai iyaka da birnin Konni a kasar Nijar

https://p.dw.com/p/3SLoF
Nigeria Soldaten in Duji
Hoto: Reuters/J. Penney

Cigaba da rufe iyakokin kasar ga alama na cigaba da sosa zukatan wasu ‘yan Najeriyar dama makwabtan kasashe, yayin da kuma a bangare daya wasu ke hamdala da daukar matakin, sakamakon alfanu da cigaba da suka bayyana sun samu. Birnin Illela a jihar Sakkwato shi ne kusan babbar mahada da ta hada Illela da kuma birnin Konni na jamhuriyar Nijar, inda ake gudanar da kai kawo na kasuwaci a ko wace ranar Lahdi a mako. To amma sai dai kuma tun bayan aiwatar da rufe iyakokin kasar, kusan lamura sun sauya.

Galibi ‘yan kasuwar wannan gari na Illela da suka saba yin kasuwacin kasa da kasa sun bayyana irin yanayin da suka fada tun bayan rufe iyakokin Najeriya. Alhaji Ibrahim Akande wani dan kasuwar sayar da motoci ya bayyanan wa DW cewa rufe iyakar ya yi matukar jawo musu asara.

Grenze Nigeria Kontrolle
Hoto: Natasha Burley/AFP/Getty Images

Zagayawar da DW ta yi a bakin wannan iyaka ta Illela da Konni, wakilinmu Maawiyya Abubakar Sadi, ya tarar dimbin motoci musamman manya da ke dakon kaya da kuma matukansu da dama da aka dakatar a bakin wannan iyaka, kuma sun bayyana masa cewa tsawon lokaci suka shafe suna a kan iyakar. 

Mafi yawancin mutanen wannan yanki na Illela da Konnin a Jamhuriyar Nijar, na bayyana cewa suna cikin wani hali inda kasuwacin yake samun koma baya, yayinda su kuma jami’an hana fasa kwauri da na shige da fice, ke cigaba da kwace duk wani abun da aka yi yunkurin shigowa ko fita da shi a kasashen biyu. To amma kuma a gefe guda galibin manoma musamman ma na shinkafa wadanda DW tab zanta da sun bayyana cewa su kam daukar matakin gaba ta kaisu.

Idan dai ba’a manta ba, gwamnatin Najeriyar ta rufe iyakokin kasar tun a farkon watan Oktoba, bisa a wani mataki na inganta fannin noma da kuma samar da tsaron kasa a cewar gwamnatin.